Zelensky na fatan kawo karshen yaki da Rasha a 2025

A ranar Juma'a shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana fatan kawo karshen yaki da kasarsa ke yi da Rasha a shekara mai zuwa ta 2025.

Mista Zelensky ya fadi hakan ne yayin da yake jawabi a ziyarar da ya kai birnin Berlin na Jamus domin neman ci gaba da samun tallafin kasar.

A yayin da sojojin Ukraine ke shirin sake shafe wani sabon lokacin hunturu a fagen daga, shugaban nasu na ci gaba da neman tallafi a ziyarar kwanaki biyu da yake yi a Tarayyar Turai inda tuni ya je biranen London da Paris da kuma Rome.

Karin bayani: Ukraine ta jaddada aniyarta ta tattauna da Rasha

 A ziyarar tasa ga shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, Zelenskey ya sanya tufafin nan da aka saba ganinsa da su na soji, sannan ya nuna godiyarsa ga Jamus bisa tallafin da ta ke bai wa kasarsa, tare da neman kar Jamus ta rage wani abu na tallafin a shekara mai kamawa.

Karin bayani:Rasha ta bukaci Ukraine ta mika wuya don samun zaman lafiya

Shugaban ya kuma nuna fatan kawo karshen yaki tsakanin Ukraine da Rasha a shekara mai zuwa ta 2025 tare da gabatar da kudurinsa na cin nasara a kan kasar ta Rasha.

Kafun isarsa Jamus shugaba Zelensky ya ziyarci Fafaroma Francis a fadarsa ta Vatican domin ci gaba da neman goyon baya ga kasarsa.


News Source:   DW (dw.com)