Wani harin makami mai linzami na Rasha da ya fada Vinnytsia a kasar Ukraine ya hallaka akalla mutum 20 tare da jikata wasu mutane 90 a cewar hukumomin na Ukraine.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya baiyana harin a matsayin aikin ta'addanci a kan jama'a fararen hula.
Yan sandan Ukraine sun ce makamai masu linzami guda uku da aka harba sun lalata gine gine da dama.
Hukumomin na Ukraine sun ce kullum Rasha na kai hari kan fararen hula tare da hallaka kananan yara