Sa'o'i bayan kisan 'yar jarida Shireen Abu Akleh ne dai shahararriyar kafar yada labaran ta AlJazeera da take yi wa aiki kafin ajalin nata, ta dora alhakin kisan da ta kira na gilla kan rundunar sojojin Isra'ila. Aljazeera ta fidda wannan sanarwar cike da alhini, bayan da bangaren Falasdinawa ya dora alhakin kisan gillar kan sojojin Isra'ila a yayin da sojin Isra'ila ke nuna yiwuwar Falasdinawa ne suka harbe ta a yayin da suke musayar wuta a tsakaninsu. Shireen na kan aikin tattara rahoto a lokacin da ta gamu da ajalinta a Gabar Yamma da Kogin Jordan, ta kwashe fiye da shekaru 25 tana aikin aika wa tashar ta Aljazeera rahotann. Shireen dai, ta rasu tana da shekaru 51 a duniya.
Kafar yada labarai ta Aljazeera ta dora alhakin kisan gillar da aka yi wa 'yar jarida Shireen Abu Akleh a yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan, kan rundunar sojojin Isra'ila.