Dubban al'ummar Mozambique sun fito kan titunan Maputo babban birnin kasar domin nuna goyon baya ga madugun adawa Venancio Mondlane tare kuma da yin tir da sakamakon zaben kasar da aka gudanar a ranar tara ga watan Oktoba.
Karin bayani: Rikicin game da sakamakon zaben Mozambik
Wannan zanga-zangar na zuwa ne bayan share makonni na bore da ya biyo bayan zaben shugaban kasa, wanda aka ayyana dan takarar jama'iyya mai mulki ta Frelimo a matsayin wanda ya yi nasara. Madugun adawa da ya kira zanga-zangar ya ce ba yana so ya kwaci mulki da karfi ba ne, amma ya sha alwashin ci gaba da gwagwarmaya har sai an dawo da gaskiya da adalci.
Karin bayani: Afirka ta Kudu ta garkame iyakarta da Mozambik
Dama dai a jajibirin zanga-zangar kungiyar lauyoyi ta Mozambique ta yi gargadi a game da barkewar gagarumin tashin hankali da ka iya haifar da zubar da jin a kasar, tare da yin kira da a kawo batun rushe zaben.