Wannan bayani na kunshe ne a jawabin da mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya yi a inda ya tabbatar da cewa gwamnati ta karbi tuban dan bindigar.
Mataimakin gwamnan Hassan Nasiha ya ce tun bayan da suka cimma matsaya, yanzu haka sama da makwanni 6 ke nan ba a sami asarar rai ba a jihar a sabili da ayyukan 'yan ta'addan.
A watan Yunin da ya gabata ne gwamnan jihar ta Zamfara Bello Mohammed Matawalle ya umurci mataimakinsa da ya jagoranci tattaunawar sulhu da 'yan bindigar, yanzu haka Turji na bukatar a sako masa 'yan bindigan da ke hannun gwamnati da ma kawo karshen kisan da ya ce ana yi wa fulani 'yan uwansa.