Zaman makoki a Burkina Faso

Zaman makoki a Burkina Faso
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na Burkina Faso, Laftanar Kanar Paul Henri Sandaogo ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar. Bayan harin ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 79.

A daren Asabar zuwa Lahadi wasu mutane dauke da makamai suka kashe  fararen hulan a wani hari da suka kai a kauyen Seytenga dake a rewacin Burkina Fason kan iyaka da Nijar. Koi'na a cikin ofisoshi gwamatin na cikin gida da ketare an yi kasa-kasa da tuttocin kasar domin girmama wadanda suka mutu.Wanda ke daya daga cikin hare-hare mafi muni da aka kai, tun bayan da sojoji suka karbi mulki a cikin watan Janairun da ya gabata.

 


News Source:   DW (dw.com)