Zaman lafiya a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Ministocin harkokin wajen kasashen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Ruwanda sun jaddada muhimmancin ci gaba da girmamama yarjejejiyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin da ke riki a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Ministocin sun gana tare da ministan harkokin wajen Angola a birnin Goma fadar lardin arewacin Kivu na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, inda aka kaddamar da kwamiti tsakanin kasashen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Ruwanda domin kula da shirin samar da zaman lafiya a yankin.

Karin Baynai: Gabashin Jamhuriyar Demokaradiyya Kwango cikin halin yaki

An kulla yarjejenyiar tsakanin dakarun Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da 'yan tawayen kungiyar M23 mai samun goyon bayan Ruwanda. Shi dai Tete Antonio ministan harkokin wajen kasar Angola ya tabbatar da wannan bayanan bayan ganawa tsakanin manyan jami'an diflomasiyyan kasashen.

Ita dai Therese Kayikwamba Wagner ministar harkokin wajen kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ba ta ce komai ba bayan wannan ganawa.

 


News Source:   DW (dw.com)