Ma'aikatan agaji na ci gaba da aikin nemo wasu da ake zaton bola ta rufta da su a Yuganda. Jami'ai a Kampla sun ce a yanzu haka an kwantar da kimanin wasu mutane 14 a asibiti, bayan da aka ceto su. Kana Hukumomi na cewa, iftila'in ya auku ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka tafka a ranar Jumma'ar da ta gabata.
An kwashe tsawon gomman shekaru ana zuba datti a babban ramin zuba sharar da ake kira da Kiteezi, da aka yi gargadin cewa akwai barazanar ya zaftare. Mazauna yankin na ci gaba da nuna damuwa kan dumamar yanayi da kuma illa ga lafiyarsu da wurin zai iya haifar wa.