Hukumomin kasar Kamaru sun tabbatar da mutuwar mutane hudu, yayin da wasu 50 kuma suka yi batan dabo, bayan kifewar motoci 3 dauke da fasinjoji, sandiyyar zaftarewar kasa a yammacin kasar.
Yayin ziyara a wurin da lamarin ya faru, ministan ayyuka na kasar Emmanuel Nganou Djoumessi, ya ce ruwan sama mai karfi da aka samu a kasar ranar Talata shi ne ya janyo zaftarewar kasar, a kan babban hanyar da Dschang, da ke hadewa da Douala cibiyar kasuwancin Kamaru.
Karin bayani:Kamaru ta hana magana kan rashin lafiyar Paul Biya
Ministan ya umarci a mika gawarwakin mutane hudun da aka gano zuwa wajen ajiyarsu, kuma a bai wa wadanda suka samu raunuka kulawar gaggawa don ceto rayukansu, sannan kuma masu aikin agaji su ci gaba da laluben sauran mutane hamsin din da suka bace.