Zaben Osun APC da PDP na kankankan

Zaben Osun APC da PDP na kankankan
A Najeriya fafatawa na kara tsanani tsakanin jam'iyyar APC da babbar jam'iyyar adawa ta PDP a zaben gwamnan jihar Osun da ake gudanarwa a Kudu maso yammacin kasar

Ya zuwa yanzu komai na tafiya daidai a zaben gwamnan jihar Osun a yankin Kudu maso yammacin Najeriya da ke gudana a wannan Asabar.

Wakilin DW Mansur Bala bello ya ce "Zaben na tafiya a cikin tsanaki da kwanciyar hankali, sai dai zargin amfani da kudi ya mamaye bakunan 'yan siyasa." Rahotanni sun ce ana kankankan a zaben gwamnan da ke gudana tsakanin jam'iyyar APC da PDP.

Tun daga farko hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, ta ce ta isar da komai a cikin lokaci kafin da sanyin safiyar yau a bude runfunan kada kuri'ar, ana kuma hasashen fiye da mutane miliyan daya da rabi za su fito domin zabar sabon gwamna.

Zaben na zaman zakaran gwaji dafi ga babban zaben Najeriya na 2023 da ke tafe nan kasa da watanni bakwai masu zuwa.

Hukumomin tsaron kasar Najeriyar dai sun tanadi matakan tsaro a wani mataki na hada barkwewar rikici a daura da abubuwan dfa suka faru a gabanin wannan Asabar.


News Source:   DW (dw.com)