Zaben kasar Kenya ya bar baya da kura

Zaben kasar Kenya ya bar baya da kura
Zanga-zanga ta barke a yankin Kisumu da ma wasu yankunan birnin Nairobi fadar gwamnatin kasar Kenya, bayan da sanar da sakamakon zaben shugaban kasa.

Masu bore na tayar da jijiyoyin wuya da kuma ikirarin an tafka magudi a zaben kasar Kenya, inda tuni suka fara kone-konen tayoyi da kuma datse wasu hanyoyi. Sai dai kuma jami'an 'yan sanda sun harba barkonon tsohuwa a wani mataki na tarwatsa masu zanga-zangar. 

Kawo yanzu dai madugun adawar kasar, Raila Odinga mai kimanin shekaru 77, bai fito ya ce komai ba dangane da sakamakon zaben da ya bai wa mataimakin shugaban kasar William Ruto nasara, ko da yake ya sha ikirarin cewa ana kwarar sa a zabuka hudu da ya tsaya takara a baya.

A yanzu haka dai 'yan kasar na jira su ga ko Mr. Odinga da ya sha kaye zai kai kara kotu domin kalubalantar sakamakon zaben da aka gudanar cikin lumana.


News Source:   DW (dw.com)