Zaben Botswana: Masisi na neman wa'adi na biyu

Jam'iyyar Botswana Democratic Party BDP ta kasance kan mulki na tsawon shekaru 58, tun lokacin da kasar ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin mallakar Burtaniya a 1966. Zaben da za a karkare shi a kwana guda zai tabbatar da nasarar shugaba mai ci Mokgweetsi Masisi 'dan shekaru 63 da ke neman wa'adin mulki na biyu ko kuma akasin hakan. Kazalika baya ga zaben kujarar shugabancin kasar za kuma a zabi 'yan majalisar dokoki daga lardunan kasar.

Karin bayani: Botswana: Masisi ya zama shugaban kasa 

'Yan takara uku su ne ke kan gaba wajen kalubalantar shugaba Masisi da suka hada da Duma Boko na jam'iyyar UDC da Dumelang Saleshando na BCP da kuma Mephato Reatile na jam'iyyar Botswana Patriotic Front. A dai wannan rana ake sa ran fara sanar da sakamako ina a 'yan kwanaki masu zuwa ake sa ran sanar da sakamakon zaben a hukumance.

Karin bayani: Botswana: Jam'iyya mai mulki ta lashe babban zabe 

Botswana dai ta kasasnce kasar da ke bin tsarin dimukuradiyya sau da kafa a nahiyar Afirka kuma ake gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da tashin-tashina ba.

 


News Source:   DW (dw.com)