Za a sami karuwar fari a yankin kahon Afirka

Za a sami karuwar fari a yankin kahon Afirka
Rashin isashen ruwan sama a damina biyar a jere da yankin kahon Afirka ke fuskanta na barazanar samun karuwar fari a yankin.

Hukumar hasashen yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai yiwuwar karuwar fari kan wanda yankin kahon Afirka ke fuskanta a yanzu.

Yankin da yanzu haka ke fuskantar mumunan fari da ba a ga irin shi ba sama da shekaru 40, da kuma damina karo na biyar da ake samun karancin ruwan sama, farin zai kazanta a nan gaba a cewar mai magana da yawun hukumar Clare Nullis.


Kasashen Ethiopia da Kenya da Somalia na daga cikin kasashen da farin zai kara ta'azzara sabili da rashin ruwa. Hukumar ta ce wannan mataki na nuna bukatar samun karin agajin gagawa musamman a wadannan kasashen.
 


News Source:   DW (dw.com)