Sakamakon sake bullar annobar a china hukumomin sun tilasta wa jama'a zaman gida tun a cikin watan Afrilun da ya gabata musammun ma a birnin na Shanghai cibiyar tattalin arzikin kasar mai yawan al''umma miliyan 25. Gwamnatin ta China ta ce an fara samun saukin cutar don haka, an dage haramci da dama da aka yi na takaita walwalar jama'a.