Za a sake bude filin jirgin saman birnin Damascus na Syria

Hukumomi a kasar Syria sun sanar da cewa a ranar Talata mai zuwa 7 ga wannan wata na Janairu, za a bude filin jirgin saman birnin Damascus, don fara jigilar fasinjoji na cikin gida da ketare, sakamakon daidaituwar al'amura bayan hambarar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad a cikin watan Disamban shekarar da muka yi ban kwana da ita ta 2024.

Karin bayani:'Yan tawaye sun karbe kasar Syria inda shugaba Assad ya arce

Shugaban hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasar Ashad Al Saliby ne ya tabbatar da hakan a Asabar din nan, kamar yadda kafar yada labaran Syria mai suna SANA ta rawaito.

A ranar 8 ga watan Disamban bara ne 'yan tawayen HTS suka tabbatar da kawar da Bashar Assad daga kan kujerar mulkin Syria, bayan shafe tsawon shekaru 13 ana yakin basasa da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu dari shida.

Karin bayani:Ko sabbin shugabanin Siriya za su yi dimukaradiyya?

Tuni dai jami'an diflomasiyya daga kasashe daban-daban suka fara kai ziyara kasar don ganawa da sabbin mahukuntanta, kuma kamfanin sufurin jiragen kasar Qatar ya sanar da cewa zai koma jigilar fasinjoji a Damascus, bayan kaurace wa kasar tsawon shekaru 13.


News Source:   DW (dw.com)