'Za a kafa gwamnatin rikon kwarya a Sudan'

Shugaban Rundunar Sojin Sudan ya ce nan ba da jimawa ba za a samar da gwamnatin rikon kwarya a kasar a yayin da sojinsa ke samun nasara a kan abokan gabansu na RSF a babban birni da kuma tsakiyar kasar da yaki ya yayyaga.

A yayin da ya ke magana a birnin Port Sudan dake gabar teku inda gwamnatinsa ke gudanar da aiki, Abdel Fattah al-Burhan ya ce gwamnatin na rikon kwarya zai kunshi kwararru masu zaman kansu.

Sojojin Sudan na kara samun galaba a kan dakarun RSF

al-Burhan ya ce gwamnatin na rikon kwarya zai kunshi kwararru masu zaman kansu kuma babban makasudin kafa gwamnatin shi ne taimakawa wajen karasar da aikin da sojin suka fara tare da raba Sudan da mayakan kar ta kwana na RSF.

Hafsan sojin ya kuma nuna cewa gwamnatin na rikon kwarya zai share fili da sauya fasalin siyasar kasar wanda zai kai ga shirya zabe.

Yan tawayen RSF a Sudan sun kashe akalla mutum 60 a Omdurman

Ya kuma ce za a amince da samar da kundin tsarin mulki kafun nada Firaminsta sannan ya yi alkawarin ba zai sa baki ko katsalanda ga aikin Firaministan ba.


News Source:   DW (dw.com)