Za a binciki sahihancin zaben Namibiya

Hukuncin kotun ya biyu bayan karar da manyan jam'iyyun adawar Namibiya suka shigar na zargin tafka magudi a zaben, da ya bai wa jam'iyya mai mulki ta SWAPO nasara. Daga cikin binciken da za a gudanar bisa umurnin kotu, har da adadin kuru'un da aka kada aka kuma kirga a kowace mazaba, a dukannin ranakun da aka yi dakon sakamako. An dai ruwaito cewa, an samu karancin takardun kada kuri'a da tangardar na'urori a wasu wuraren, kana aka dage zaben a wasu mazabun.

Tuni dai zababbiyar shugabar kasar, Netumbo Nandi-Ndaitwah ta yi watsi da zargin 'yan adawan tare da kara jadadda cewa an gudanar da zaben ne bisa aminci da gaskiya. Jam'iyyar SWAPO ta kwashe tsawon shekaru 34 tana mulki a kasar ta Namibiya da ke Kudancin Afirka.

 


News Source:   DW (dw.com)