A cikin wata sanrwar da ta fitar, ma'aikatar tsaron ta Birtaniya ta ce jiragen na iya nuta mai cin dogon zango har mita 100 a kasa, kana kuma ana iya amfani da su a wuraren da ke sa sassaucin zurfi na ruwan teku a cikin hanzari.
Ko baya ga kyautar jiragen guda shida, Birtaniya ta kuma sha alwashin horar da jami'an sojin Ukraine yadda za su amfani da sabbin makamai a wani mataki na kare kansu daga mamayar Rasha.
Ana dai zargin ko akwai yiwuwar Rasha ta binne manyan nakiyoyi a karkashin tekun Ukraine don hadasa tarnaki wa gabar ruwa Bahar Aswad da Ukraine ke amfani da ita wajen fitar da kayayakin abinci da take nomawa zuwa kasuwannin duniya.