Yuganda: Kotu ta daure Kizza Besigy

Yuganda: Kotu ta daure Kizza Besigy
Wata kotu a Yuganda ta daure daya daga cikin shugabannin yan adawar kasar a gidan kurku Kizza Besigye, bayan da ta sameshi da laifin tada zaune tsaye da tunzura jama'a.

An sake kama Besigye, wanda ya yi takarar shugaban kasa har sau hudu a ranar Talata, mako guda da sakinsa. Kizza Besigye mai shekaru 66 a duniya, wanda ya yi kaurin suna wajen caccakar shugaba Yoweri Museveni, ya jagoranci zanga-zanga da dama a kwanakin baya-baya nan don nuna adawa da tsadar rayuwa da ta addabi Uganda sakamakon yakin Ukraine. Nan gaba ne kotun za ta bayyana hukuncin da ta yanke masa.

 


News Source:   DW (dw.com)