Yemen: Karya yarjejeniyar tsagaita wuta

Yemen: Karya yarjejeniyar tsagaita wuta
Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton mutuwar fararen hula guda 19 a Kasar Yemen yayin da wasu 32 suka jikkata.

Duk da shirin tsagaita bude wuta na tsawon watanni biyu da aka sabunta,MDD ta ce  akasarin wadanda suka mutu an kai musu hare-hare na bam ko kuma sun taka nakiyoyin da aka dadassa. Kasar ta Yemen da ta fi kowacce talauci a yankin Larabawa ta shafe fiye da shekaru bakwai tana fama da rikici tsakanin 'yan tawayen Houthi, da ke kusa da Iran, da dakarun gwamnati, da ke samun goyon baya Saudiyya da kawayenta.Yakin dai  ya yi sanadiyyar mutuwar dubban darurruwan mutane tare da raba wasu miliyoyi da matsugunansu.

 


News Source:   DW (dw.com)