A wannan Lahadin ce yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta fara aiki a Gaza wanda ya dakatar da yakin da aka kwashe tsawon watannin 15 a gabzawa a Zirin. Sai dai kuma Ministan harkokin wajen Isra'ila, Gideon Saar ya yi gargadin cewa, yankin Gabas ta Tsakiya ba zai samu kwanciyar hankali ba, idan har kungiyar Hamas ta ci gaba kasancewa kan madafun ikon Gaza.
Karin bayani: Yaushe za a tsagaita wuta a Gaza?
Da yake magana kan yarjejeniyar zaman lafiyar da ta fara aiki, Saar ya ce Isra'ila na da kudurin cimma dukannin manufofinta na yakin da take yi da Hamas, ciki har da rusa karfin gwamnatinta.
A gefe guda, hukumar bayar da agajin Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA, ta ce tana da tireloli kimanin 4,000 shake da abinci da kuma kayan agaji da suke shirya shiga Zirin Gaza. Kwamhisnan hukumar, Philippe Lazzarini ya bayyana kyakyawan fatan da yake da shi, kan yadda shigar da kayan agajin zuwa Zirin zai rage matsalar jin kai da ya ta'azzara a yankin.
Karin bayani: Za a shigar da kayayakin agaji a Zirin Gaza
Har wayau, kafar yada labaran birnin Alkahiran Masar ya ruwaito cewa, kimanin motoci 160 dauke da kayan agaji suka shiga yankin Rafahna Gaza domin isar da su zuwa yankin Shalom da ke karkashin ikon Isra'ila. Daga cikin motocin, shida na dauke ne da man fetur.