Shugaban Amirka Joe Biden da Firaministan Israila Yair Lapid sun tattauna hanzarin da ake samu a yunkurin Iran kan shirinta na makamashin nukiliya inda shugaban Israila ya ci alwashin Iran ba za taba mallakar makamin nukiliya ba.
Shugaban Amirka wanda ke shirin kai ziyara kasar Saudiyya a ranar Juma'a ya jaddada wa Lapid muhimmancin da ake akwai ga Israila ta sami hadin kai da sauran kasashe da ke yankin na Gabas ta Tsakiya.
Tattaunawar shugabannin biyu na zama jigon ziyarar sa'oi 48 da Biden ya kai da nufin karfafa dangantakar da ke tsakanin Amirka da Israila.
Ana sa ran shugabannin za su rattaba hannu akan wani kudiri da zai karfafa kawancen tsaro da kuma kudirin ganin Iran wadda Israila ke dauka a matsayin abokiyar gaba bata mallaki makamin nukiliya ba.