Yan tawayen RSF a Sudan sun kashe akalla mutum 60 a Omdurman

Mutane akalla 54 ne suka mutu a yayinda dakarun rundunar kar-ta-kwana ta RSF ta kai mummunar farmaki kasuwar Omdurman da ke wajen birnin Khartoum, inda wasu mutane kimanin 158 suka samu raunuka.

Karin bayani: An kashe mutum 70 a asibitin Sudan

Harin da RSF ta kai a wannan rana ta Asabar 1 ga watan Fabrairu, 2025 na daya daga cikin hare-hare mafi muni da dakarun sojojin sa-kan suka kaddamar a baya bayan nan, duk da cewa babu wata sanarwa daga RSF kan wannan farmaki da aka kai kasuwar Sabrein da ke birnin Omdurman.

Karin bayani: Sojojin Sudan na samun nasara kan 'yan tawayen RSF 

Kakakin gwamnatin Sudan kuma ministan bunkasa al'adu Khalid al-Aleisir, ya yi tir da wannan mummunar hari da ya yi sanadiyyar rayukan mata da kananan yara da dama.

.


News Source:   DW (dw.com)