Mazauna yankin suka ce sun ji karar harbe-harbe a kewayen yankin Nyiragongo, inda aka kai wa sojojin Kwango hari, lamarin da ya jikkata mutane biyu. Tun a jiya Litinin ne kasar Ruwanda ta ce wasu fararen hula sun jikkata sakamakon makamin roka da da aka harba daga Kwango zuwa wani yanki na iyakar kasarta da Kwango, kuma ta yi kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa kan lamarin.
Sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta zargi kungiyar M23 da kai wannan hari. Dangantaka tsakanin Kwango da Ruwanda ta yi tsami tun bayan kisan kiyashin da aka yi a Ruwanda a shekarar 1994. musamman ma bayan da 'yan Hutu da ake zargi da neman murkushe 'yan Tutsi suka samu mafaka a Kwango.