Jaridar Faransa ta Le Monde ita ce ta wallafa labarin da ke cewa 'yan tawayen na Abzinawa da ke gwagwarmaya da makamai na amfani da jirage marasa matuka na Ukraine domin kai hare-hare a wasu sassan Mali, kamar yadda suma sojojin Malin ke samun goyon bayan daga sojojin hayan kamfanin Wagner na Rasha.
Karin bayani: Rasha ta kakkabo jiragen Ukraine marasa matuka
Ministan Harkokin Wajen Ukraine ya musanta zargin da jaridar Le Monde ta wallafa na ba wa 'yan tawayen jirage marasa matuka samfurin UAV. A watan Augutan 2024, Mali ta yanke huldar diflomasiyya da Ukraine bisa zargin tallafawa 'yan tawayen da makamai wanda ya kai su ga halaka sojojin Mali da dama da kuma wasu sojojin hayan Rasha na Wagner a yankin arewacin Mali.