'Yan ta'addar Mali sun kama mayakin Wagner

'Yan ta'addar Mali sun kama mayakin Wagner
Wannan shi ne karon farko da gamayyar GSIM ta 'yan ta'addar Mali mai alaka da kungiyar Al-Qaeda da ke ikirarin jihadi a kasashen Sahel ta ce ta kama wani jami'in kamfanin Wagner mallakin kasar Rasha. 

Babbar gamayyar 'yan ta'addan kasar Mali da ake yi wa lakabi da GSIM, ta ce ta kama wani mayaki na kamfanin tsaron Rasha wato Wagner Group da Mali ke alaka da shi. Wannan ikirari na cikin wata sanarwa da gamayyar 'yan ta'addar ta aike wa kamfanin diillancin labaran Faransa, AFP, ba tare da wata hujja da ke tabbatar da hakan ba.  

Tun da farko alakar da Mali ke yi da kamfanin na Rasha ce ta farraka kan hukumomin Malin da uwar gijiyar kasar, Faransa da sauran manyan kasashen duniya irinsu Amurka. Mahukuntan Bamako sun ce kamfanin na Wagner na horas da sojojin kasar ne, a yayin da Kasashen Yamma ke zargin gwamnatin mulkin sojin Mali ta yi kwangilar kamfanin na Wagner domin ya yi mata aiki a matsayin sojan haya.


News Source:   DW (dw.com)