'Yan ta'addan JNIM sun yi ikrarin kai hari mafi muni a Benin

Kungiya da ke da alaka da al-Qaeda taJNIM ta dauki alhakin harin ta'addanci da aka kai a arewacin kasar Benin mai iyakar kasar da Burkina Faso da Nijar, harin da ya hallaka sojoji 28 a tsakiyar wannan makon.

Karin bayani : Kemi Seba zai tsaya takara a Benin

Harin da ke zama mafi muni da sojojin kasar Benin din suka gani a baya-bayan nan na zuwa ne, a daidai lokacin ma'aikatar tsaron Benin ta kara yawan sojojin da ke sintiri kan iyakar kasar da makwabtanta irinsu Nijar da Burkina Faso, wanda suka jima suna fama da ayyuklan ta'addanci.

A cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar JNIM mai alaka da al-Qaeda ta bayyana hallaka sama da sojoji 30 tare da kwace bindigogi da jirage marasa matuka da tankokin yaki.

Karin bayani : Benin: Kokarin sasanta rikici da Nijar

Wata majiya daga kasar ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar daga shekarar 2021 ya zuwa watan Disambar 2024 sama da sojoji 120 ne 'yan ta'adda suka kashe a kasar.


News Source:   DW (dw.com)