Rundunar Sojin Masar na cewa kimanin dakarunta 11 aka kashe a wani harin da 'yan ta'adda suka kai gabashin mashigar ruwan Suez da ke Sinai. A cewar kakakin rundunar sojin kasar Kanal Ghareeb Abdul Hafez, masu tayar da kayar bayan sun kai harin ne babban madatsar ruwan kasar wanda ya haifar da arangama tsakaninsu da dakarun. Baya ga jami'an sojin 11 da suka rasa rayukansu, wasu biyar sun jikata yayin musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.
Kanal Abdul Hafez ya ce tuni suka baza komarsu wajen neman 'yan ta'addan. Kasar Masar na fama da hare-haren masu matsanancin ra'ayi galibi a yankin na Sinai tun daga shekarar 2013, a lokacin da sojoji suka hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Mohammed Morsi da ke zama shugaban kasar na farko da aka zaba a kan tafarkin dimukaradiyya. Tun daga wancan lokacin daruruwan jami'an tsaro ne suka mutu a hare-haren 'yan ta'addan da ke da alaka da kungiyar IS a kasar da ke arewacin nahiyar Afirka.