'Yan Shi'a na zanga-zanga a Iraki

'Yan Shi'a na zanga-zanga  a Iraki
'Yan gwagwarmaya a Iraki sun kwashe daren ranar Asabar a cikin ginin majalisar dokoki da ke Bagadaza, inda suke neman dole a kawo sauye-sauye a tsarin gudanar da kasar.

Magoya bayan Moqtada al-Sadr, fitaccen malamin nan na Shi'a a Iraki sun kwashe daren da ya gabata cikin majalisar dokoki da ke Bagadaza babban birnin kasar, wani abu da ke nuna girman gwagwarmayar neman kawo sauyi da aka kwashe watanni ana yi.

Su dai 'yan Shi'ar na Iraki da ke zanga-zanga, suna neman kawo karshen cin hanci da rashawa ne a harkokin gwamnati.

Haka ma sun ce sai an yi watsi da Mohammed Shi'a al-Sudani da aka bayyana sunansa a matsayin wanda zai zama firaminista.

Masu zanga-zangar sun kuma lashi takobin ci gaba da zaman dirshen a majalisar har sai yadda hali ya yi a kokarin tilasta mahukuntan Iraki tabbatar da garambawul da suke neman gani an yi a tsarin gudanar da mulki na kasar.

Da dama daga cikin 'yan Irakin dai na cewa sun dawo daga rakiyar 'yan siyasa a yanzu.


News Source:   DW (dw.com)