'Yan sandan Kenya sun harba hayaki mai sa hawaye don tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga da suka fantsama kan titunan Nairobi babban birnin kasar a wannan Talata, wadanda ke nuna fushinsu kan yawan kisan da ake yi wa mata a kasar ba gaira ba dalili.
Karin bayani:'Yan sanda sun haramta zanga-zanga a tsakiyar birnin Nairobi
Kimanin mata 300 ne suka shiga zanga-zangar suna kirarin cewa a kawo karshen kisan gillar da ake yi wa mata ba gaira ba dalili, inda 'yan sandan suka kama mutane 3.
Karin bayani:Gomman masu zanga-zanga sun mutu a Kenya
Zanga-zangar dai ta kasance ta lumana, dalilin da ya sa al'ummar kasar ke mamakin yadda 'yan sanda suka far wa mutanen, kuma 'yan sandan ba su yi wani karin haske a kai ba.