Rundunar 'yan sandan Ghana ta cafke jagoran masu zanga-zangar adawa da hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba Oliver Barker-Vormawor, tare da wasu mukarrabansa uku, kwana guda bayan kama mutane 42 da suka yi arangama da 'yan sandan a Accra babban birnin kasar.
Karin bayani:Fargaba gabanin babban zabe a Ghana
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Ghana Grace Ansah-Akrofi, ta ce sun kama Mr Oliver Barker-Vormawor bisa aikata laifukan da suka saba wa dokokin kasar, ta inda suka far wa 'yan sanda a daidai lokacin da suke tsaka da aikinsu na wanzar da zaman lafiya a kasar.
Karin bayani:Cece-kuce gabanin zaben shugaban kasar Ghana
Zanga-zangar wadda kungiyar nan mai rajin kare dimukuradiyya da yaki da tsadar rayuwa ta Democracy Hub ta shirya, ta barke ne a ranar Juma'ar da ta gabata sannan ta karkare a jiya Lititin.
Matasan da ke zanga-zangar sun koka matuka da yadda tsadar rayuwa ke kara kamari a kasar, sakamakon tabarbarewar tattalin arziki, sai kuma yadda masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba ke gurbata muhalli.