Hukumar 'yan sandan ta kama Aminu Lawal wanda aka fi sani da Kano da kuma Murtala Dawu wanda aka fi sani da Mugala kan zargin su da hannu a harin da aka kai da makamai a makarantar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani jami'in makarantar. Za'a gurfanar da su a gaban kotu idan 'yan sanda sun kammala bincike.
Idan ba a manta ba, 'yan bindigar sun saki mutane 14 cikin mutane 20 da suka yi garkuwa da su bayan kwanaki 40 da sace su, sun kashe mutane biyar don tilastawa iyalai da gwamnati biyan kudin fansa.
Yanzu haka dai akwai akalla 'yan makaranta 1,500 a hannun masu garkuwa da mutane, inda dalibai 16 suka rasa rayukansu a cewar Asusun kula da Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF.