Bisa ga tsarin kasar Amurka, wajibi ne majalisun wakilai da na dattawa su amince da kasafin 2025 a karshen Satumba, idan ba haka ba miliyoyin ma'aikatan gwamnati na iya rasa aikinsu yayin da a daya bangaren za a dakatar da taimako ga marasa galihu da ma dai zirga-zirgar wasu jiragen sama sakamkon rashin kudi. Fiye da 'yan jam'iyyar Republican 12 ne suka bi sahun 'yan jam'iyyar Democrat wajen kin amince da tsawaita kasafin kudin har zuwa watan Maris na shekarar 2025, wato har bayan dan takarar da aka zaba a zaben shugaban kasa na ranar 5 ga watan Nuwamba ya hau kan karagar mulki.
Karin bayani:An cimma matsaya kan kasafin kudin Amurka
Dama dai dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump ya yi barazanar kawo tseko a matakin tsawaita kasafin kudin Amurka, matikar da ba a yi amfani da wannan dama wajen amincewa da kudirin dokar nuna shaidar zama dan kasa lokacin kada kuri'a ba. Sai dai gwamnatin Joe Biden na adawa da wannan mataki, tana mai cewa babu wata shaida da ke nuna cewa baki za su iya taka rawa a zabe mai zuwa.