Yan kasashen waje daga Turai da nahiyaar Asiya da kuma Gabas ta Tsakiya na ficewa daga Lebanon a yayin da Israila ke ci gaba da luguden bama bamai a Beirut babban birnin kasar. A waje guda dai gwamnatoci a fadin duniya sun bukaci yan kasashensu su fice daga Lebanon.
Wasu kasashen sun samar da jirage domin kwashe mutanensu a wasu wuraren kuma daruruwa mutane na shiga jiragen ruwa da kananan kwale kwale domin ficewa.
Israila ta bukaci jama'a su kauce daga garuruwa fiye da ashirin a kudancin Lebanon a ci gaba da rikicin da ya ja Iran shiga ciki da kuma barazanar fadawar Amurka cikin rikicin.