'Yan tawayen Houthi na Yemen sun samu nasarar kakkabo wani jirgi marar matuki da Amurka ta kai musu hari da shi a Juma'ar nan a yankin al-Jawf, sakamakon yadda take ci gaba da kai hari kan jiragen ruwa na kasuwanci da ke bi ta kogin Baharmaliya, a matsayin martani ga yakin da Isra'ila ke yi a Gaza.
Karin bayani:'Yan tawayen Houthi na Yemen sun harbo jirgin yakin Amurka
Tuni dai faifan bidiyon jirgin da aka harbo ya karade shafukan sada zumunta inda aka hango shi ya turnuke da hayaki sannan ya tarwatse, kuma rundunar sojin Amurkan ta ce ta fara bincike a kan yadda lamarin ya faru.
Karin bayani:Jiragen yakin Isra'ila sun yi barin wuta a Yemen
'yan tawayen na Houthi sun mallaki makamai masu linzami na harbo jiragen sama, cikinsu har da kirar Iran mai suna 358, to amma Iran din ta sha nanata cewa bata bai wa Houthin makaman yaki.
Houthi da Hamas da kuma Hezbollah na kan gaba wajen samun taimakon kasar Iran.