Yan fashi sun kone mutum 32

Yan fashi sun kone mutum 32
Gwamnatin kasar Madagaska ta baza jami'an tsaro don farautar barayin shanun da ake zargi da laifin kashe mutum sama da talatin tare da bunka wa gidajensu wuta.

Gwamnatin kasar Madagaska ta baza jami'an tsaronta don farautar wasu da ake zargin 'yan fashin daji ne da suka kashe mutum fiye da talatin kafin daga bisani suka bunka wa gidajensu wuta. An tura jirage masu saukar ungula aikin farautar wadanda gwamnati ta kira da miyagun mutane. 

Wata majiya a kasar ta ce, tana zargin an kai wa mutanen kauyen harin ne, saboda suna kwarmata wa jami'an tsaro bayanai a game da aiyukan 'yan fashin da suka hana zaman lafiya. Kasar Madagaska na daga cikin kasashen Afirka da ke fama da tashe-tashen hankula tun bayan da ta yi kokarin magance matsalar 'yan fashin shanun.


News Source:   DW (dw.com)