Mazauna yankin Ituri na jamhuriyyar Dimokradiyyar Kwango sun zargi wasu da ake kyautata zaton masu kaifin kishin Islama da hannu a kisan mutunen fiye da goma sha takwas a garin da ke gabashin Kwango. An kai harin ne a ranar Lahadi da ta gabata, kamar yadda Jules Ngongo, wani kakakin gwamnati ya tabbatar amma ya zargi mayakan Kungiyar ADF da ke gwagwarmaya da makamai da hannu a kisan gillar. Jami'in ya kara da cewa, an shiga farautar maharan.
Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a baya-bayan nan na nuni da cewa, mayakan kungiyar sun yi sanadiyar salwantar da rayuka fiye da dubu daya da dari uku a tsakanin watan Janairun 2021 zuwa Janairun 2022.