Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA cewar wani jami'an dan sanda ya ce sun gano gawarwaki mutane kimanin hamsin da biyar a cikin wasu dazuka a lardin nan na Ituri.
Baya ga kisa da kuma fyade da 'yan bindigar suka yi, wani mazaunin Lardin ya ce maharan sun kuma kwashi kayan da mutanen kauyuka suka gudu suka bari, inda suka cinnawa gidajen wuta bayan sun kammala sace-sacen.
Tuni dai mazauna yankin suka fara zargin 'yan kungiyar nan ta CODECO da kai wannan hari, sai dai ya zuwa yanzu ba wata majiya mai zaman kanta da ta tabbbatar da wannan labari.