Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar mutane 16 sanadiyyar hare-haren 'yan bindiga biyu a yankin Kudu maso yammacin kasar, mai iyaka da kasashen Najeriya da Jamhuriyar Benin. Kafar yada labaran kasar ta ce 'yan bindigar sun tattara mutane 14 wuri guda sannnan suka bude musu wuta cikin daren ranakun 22 da kuma 23 ga Fabarairu a kauyen Dioundiou. Bayan kwanaki biyu kuma 'yan bindigar suka sake halaka mutane a kusa da garin.
Karin bayani:'Yan bindiga sun halaka mutane a iyakar Jamhuriyar Benin da Nijar
A Burkina Faso kuwa babbar kotun kasar ce ta yanke wa mutane 3 hukuncin daurin rai-da-rai bayan samunsu da laifin halaka sojoji 8 tare da raunata wasu mutane 85, sanadiyyar harin da suka kai wa shelkwatar sojojin kasar da ofishin jakadancin Faransa a Ouagadougou babban birnin kasar a cikin watan Maris na shekarar 2018, ta hanyar amfani da bindigogi da kuma tayar da bam a mota.
Ma'aikatar shari'ar kasar ta sanar da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa mutane 8 kotun ta yi wa shari'a, inda ta samu uku daga cikinsu da laifin ta'addanci da hada baki wajen aikata kisa. Yayin da aka yanke wa wasu guda 2 hukuncin daurin shekaru 10 zuwa 21, bayan samunsu da laifin samarwa 'yan ta'addar kudade, sannan aka sallami mutane biyu da aka wanke daga zargin.