'Yan bindiga sun bude wuta kan jirgin MDD a Haiti

Kamfanin dillancin labarai na AP da wasu kafafen yada labaran Amurka sun tabbatar da cewa jirgin mai dauke da mutane 18 ciki har da matukansa ya sauka lafiya a birnin na Port-au-Prince duk da barin wuta daga 'yan dabar Haitin masu dauke da makamai. Kusan dukkan birnin Port-au-Prince da kewaye na karkashin ikon 'yan daba bayan sun fatattaki dukkan 'yan sanda da sauran jami'an tsaron da ke yankin.

Kain bayani: An yi yunkurin kashe firaministan Haiti

Kasar Haiti ta fada riciki tun daga shekara ta 2021 bayan halaka shugaban kasar Jovenel Moise. Ko a farkon wannan wata na Oktobar shekara ta 2024, 'yan bindigar sun kona gidaje da dama a babban birnin kasar tare da halaka mutane sama da 70, yayinda wasu dubbai suka rasa muhallansu.


News Source:   DW (dw.com)