Shugaban Ghanan mai barin gado Nana Akufo-Addo ya bayana hakan ne, yayin jawabinsa ga kasa na karshe kafin ranar shida ga wannan wata na Janairu da zai mika mulki ga sabon zababben shugaban kasar John Dramani Mahama da ya lashe zabe a watan Disambar bara. Wannan matakin da Ghanan ta dauka dai, na zaman wani tafarki na gaba ga tattabatar da tsarin kasuwanci mara shinge da kasashen Afirkan ke son dabbaka wa.
News Source: DW (dw.com)