Mutane biyun nan da ake zargi da yunkurin kai hari harabar majalisar dokokin kasar Sweden da ke birnin Stockholm za su gurfana gaban kotu a nan Jamus a Juma'ar nan, don fuskantar tuhuma.
Karin bayani:Scholz: Za mu tsaurara doka kan hari da wuka
Wadanda ake zargin 'yan asalin kasar Afghanistan masu shekaru 30 da kuma 23, an kama su ne a jihar Thuringia ta gabashin Jamus a cikin watan Maris din da ya gabata, bayan bankado yunkurinsu na kitsa yadda za su kai farmakin harbe mutane a birnin Stockholm, a matsayin martanin kona Al'kur'ani mai girma da aka yi a Sweden a bara.
Karin bayani:Barazanar ta'addanci:'Yan sandan Munich sun karfafa tsaro a filin Allianz Arena na Bayern
Ofishin babban mai gabatar da kara na Jamus ya zargi daya daga cikin mutanen da zama mamba a kungiyar ta'addanci ta ISPK, mai tushe daga IS.