Sakamakon zaben kasar Mauritius da aka fitar a wannan Talata ya nuna cewa babbar jam'iyyar adawa ta ADC da tsohon Firaminista Navin Ramgoolam ke jagoranta ta samu kaso 62 cikin 100 na kuri'un da kada.
Karin Bayani: Firaministan Mauritius ya amince da shan kayin zaben kasar
Kafar yada labaran kasar ta ce jam'iyyar ta ADC ta lashe galibin kujerun majalisar dokokin kasar, abin da ke nuna Ramgoolam wanda ya yi wa'adi uku kan kujerar firaminista zai sake dawowa kan madafun ikon kasar. Tuni Firaminista Pravind Jugnauth na kasar ta Mauritius ya maince da shan kaye a zaben da ya gabata, inda ya ce ya yi kokarin iya abin da zai iya domin kawo ci gaba lokacin da yake rike da madafun ikon kasar.