Kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya ce jami'an 'yan sanda sun yiwa masu zanga-zangar kawanya domin kwantar da tarzoma tare kuma da tabbatar da doka da oda, duk da cewa masu gangamin sama da dubu 4,000 sun yi dafifi a birnin na Luanda ba tare da hargitsi ba, inda suke ci gaba da sukar jam'iyya mai mulki ta People's Movement for the Liberation of Angola (MPLA) da kuma shugaban kasar Joao Lourenco.
Karin bayani: Angola ta yanke shawarar ficewa daga kungiyar kasashe masu arzikin man fetur
Babbar jam'iyyar adawar kasar UNITA ita ce ta kira gangamin wacce kuma a baya ta shigar da kara kotu domin kalubalantar nasarar jam'iyya mai mulki, yayin da daga bisani kotun kolin kasar ta yi watsi da karar.
Karin bayani: Angola: Ina kadarorin da aka kwato na Isabel dos Santos?
Sakataren Jam'iyyar UNITA wacce a baya ta kasance kungiyar 'yan tawaye kafin ta rikide zuwa jam'iyya, Alvaro Chikwamanga ya shaida wa AFP cewa sun fito gangamin ne domin nuna fushinsu kan yadda ake gudanar da mulkin kama-karya a kasar.