'Yan adawa na fargabar salon mulkin danniya a Tanzaniya

Kimanin mutane 520 ne aka kama a fadin kasar, a cewar sanarwar ‘yan sanda, gabanin haramtacciyar zanga-zangar Chadema a jiya Litinin, wanda aka sa ran zai janyo dubban matasa a birnin Mbeya da ke Kudu maso Yammacin kasar.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da masu adawa da gwamnati sun fara nuna fargabar cewar, matakin da 'yan sandan suka dauka na iya nuna komawa ga tsarin zalunci na tsohon shugaban Tanzaniya John Magufuli.

Kamen dai ya zo ne duk da furucin shugabar da ta gaje shi Samia Suluhu Hassan, wadda ta sha alwashin komawa fagen siyasa tare da sassauta wasu takunkuman da aka yi wa 'yan adawa da kafafen yada labarai, ciki har da dage haramcin taron 'yan adawa na tsawon shekaru shida.

 


News Source:   DW (dw.com)