Yamen: Huthi da Saudiyya sun tsagaita wuta

Yamen: Huthi da Saudiyya sun tsagaita wuta
Bayan shafe tsawon shekaru ana gwabza yaki a Yamen 'yan tawaye sun cimma yarjejeniyar tsagaita buta wuta da kawancen sojan da kasar Saudiyya ke jagoranta.

Yarjejeniyar da aka cimma karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya za ta shafe tsawon watanni biyu ne a kasar da yaki ya daidaita, kana kuma tuni ta soma aiki wannan Asabar daya ga watan Ramadana.

Bangarorin biyu da suka aminta da tsagaita buda wuta, sun kuma yi na'am da zirga-zirgar jirage daga wasu yankuna zuwa babban birnin kasar Yamen Sanaa, baya ga bude mashigar ruwa ta Hodeida da ke yammacin kasar ga tankokin dakon danyen mai, a cewar manzo na musamman na MDD da ya shiga tsakani Hans Grundberg.


News Source:   DW (dw.com)