Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce yakin da Rasha ke yi da Ukraine na kuntata wa kasashe duniya matalauta ta fannonin rayuwa da dama.
A ganawar da ya yi da manema labaru, Antonio Guterres ya ce kasashen da a baya ke fama da kansu yanzu sun kara shiga cikin hali na matsi, a sabili da hauhawar da farashin kayayyakin masaraufi da ma na makamashi suka yi, wanda a cewar shi ire-iren wadannan kasashen basu murmure daga halin da cutar Covid-19 ta jefa su a baya ba.
Guterres dai na ganin kasashen duniya ya kamata su yi amfani da wannan matsalar wajen maida ta dama ta karkata ga makamashin da ake sabuntawa.