Shugaban ya sanar da hakan ne a daidai lokacin da kasar ke tsaka da yaki har ma da tsananin bukatar kayan agajin jinkai da kuma tunkarar kalubalen 'yan gudun hijra a kasar da yaki ya daidaita.
Karin bayani: Harin RSF a yankin Darfur na Sudan ya halaka mutane 12
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ke kiraye-kirayen tsagaita bude wuta da kuma dakatar da yakin da ake gwabzawa a yankin al-Jazira, da ke kudancin babban birnin Khartoum, wanda hakan ke shafar dubban mutanen da ke yankin.