Yaki ya tilasta yara miliyan 36,000 hijira

Yaki ya tilasta yara miliyan 36,000 hijira
Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF ya ce rikici da sauran tashe-tashen hankula a duniya a karshen shekarar 2021, sun sa yara hijira fiye da kowane lokaci tun bayan yakin duniay na 2.

A cewar sabon rahoton UNICEF, kusan kananan yara miliyan 36 da dubu 500 sun kaurace wa gidajensu, yayin da akalla yara milian 2 da dubu 800 kuma suka tagaiyara. Adadin ya nuna karuwar yara 'yan gudun hijira a duniya da kaso 2.2 tun 2020.

Rahoton ya ce adadin ya zarta kima saboda rikicin kaskashen Afganistan da Yemen, UNICEF ya ja hankalin gwanatocin kasashen duniya wajen karfafa matakan kariya ga yara 'yan gudun hijira, sai dai wadan nan alkaluman ba su hada da kasar Ukraine na inda mamayar Rasha ta tilasta musu gudun hijira.

Tun watan Fabrairun shekarar 2022, akwai wasu yara miliyan biyu 'yan gudun hijira a wasu kasashen waje, yayin da yakin ya raba wasu yara miliyan uku da muhallansu a cikin Ukraine.

Rahoton ya kara da cewa karin yara miliyan 7 da 300,000 sun rasa muhallansu a cikin shekarar 2021 saboda wasu bala'o'i. Bugu da kari, yara da iyalansu ma sun rasa matsugunansu matsanancin yanayi, kamar fari a yankin Kahon Afirka da mummunar ambaliya da aka gani a kasashen Indiya da Bangladesh da Afirka ta Kudu.

Fiye da kashi uku na yaran da suka rasa matsugunansu suna zaune a yankin kudu da hamadar sahara wato miliyan 3 da 900,000 ko kuma kashi 36 cikin 100. Wannan adadin shi ne daya bisa hudun adadin da ake samu a nahiyar  Turai da tsakiyar Asiya. Kimanin kashi biyu bisa uku na duk yara 'yan gudun hijira an sanya su a makarantun firamare, yayin da kusan kashi daya bisa uku na matasa 'yan gudun hijira na samun ilimi inji rahoton Unicef.


News Source:   DW (dw.com)