Yaki ya barke a kudancin Habasha

Yaki ya barke a kudancin Habasha
A Kasar Habasha 'yan tawaye sun kai hare-hare na tsawon sa'o'i da dama a garin Gambella da ke kudu maso yammacin kasar.

Kungiyar ‘yan tawayen Oromo ta Liberation Army  wacce ake yi wa lakabi da sunan (OLA),ta kabila mafi yawan jama'a a kasar, da gwamnatin Habasha ta ayyana a matsayin kungiyar yan ta'adda tun a watan Mayun  shekara ta 2021 ta dauki alhakin kai hari. Shugaban gwamnatin yankin, Umod Ujulu, ya ambato cewar Jami'an tsaron yankin sun yi nasarar sake kwace iko da garin Gambella da ke a gabar gokin Nilu. A  cikin watan Agustan da ya gabata  ne kungiyar ta 'yan tawayen kabbilar Oromo, OLA ta yi kawance da jam'iyyar Tigray People's Liberation Front (TPLF) jam'iyyar da ta dade tana mulkin kasar Habasha kuma ta shiga yakin a watan Nuwamba shekara ta 2020 da gwamnatin tarayya ta Firaminista  Abiy Ahmed.

 


News Source:   DW (dw.com)